Yan Sanda Za Su Sa Kafar Wando Daya Da Masu Zagi A social Media


Rundunar yansandan jihar Kano tace zata sanya kafar wando daya da ma’abota shafukan sada zumunta wadanda suke cin mutumcin jama’a da yin kalaman tayar da tinziri.

Kakakin rundunar yansandan jihar Kano, SP M M Majia Ppro Kano, yace rundunar ta shirya tsaf wajen magance wannan matsala, inda yace sam ba dai dai bane wasu tsirari su ringa amfani da wannan kafa wajen yin ‘batanci ga masu mutumci ba, yace wasu na amfani da wannan kafa wajen zagin malaman addini da shugabanni ta hanyar hada hotunan su da matan banza ko dabbobi da yin zantukan da basu kamata ba wanda hakan kan haifar da rigingimu a tsakanin al’umma.

SP Majia, ya kara da cewa rundunar zata samar da kwararrun jami’anta da suka iya amfani da wadannan kafafen sada zumunta na zamani tare da basu duk abinda ya kamata domin subi sahu da gano masu aikata wannan mummunar dabi’a ta zagi, cin mutumci da wulakanta al’umma.

Yace duk wanda aka za’a dauki matakin ladabtarwa akan shi, ko dai aja masa kunne tare da gargadi, ko kuma a gurfanar da ko waye a gaban kotu domin ya girbe abinda ya shuka.

Daga karshe yaja hankalin ma’abota wadannan shafuka na sada zumunta da suyi amfani da su ta,hanyar da ya dace ba tare da sunci mutumci kowa ba, kuma su sani ko da hukuma bata kama su ba, to Allah yana kallon su da duk abinda suke aikatawa na alkairi ko na sharri kuma baza su tserewa kamun shi ba.

You may also like