Yan sandan Najeriya na gallazawa jama’a


boko_0_0

 

 

Kungiyar Amnesty International ta zargi wani reshe na rundunar ‘yan Sandan Najeriya da ake kira SARS da azabtar da mutane da kuma karbar cin hanci kafin sakin wadanda ake zargi da aikata laifufuka.

Kungiyar tayi zargin cewar, mutanen da ‘yan sandan dake yaki da ‘yan fashi  ya kama na fuskantar azabtarwa, ko horo na rataya, yunwa, ko barazanar harbesu, har sai sun amsa laifin da ake tuhumar su ko kuma su biya makudan kudade kafin a sake su.

Wani matashi mai suna Chidi Oluchi da aka kama a Enugu yace ya sha dan Karen duka kafin ya biya naira 25,500 a sake shi.

Rahoton kungiyar na yau laraba ya biyo bayan bayyanan da tace ta tattara daga mutanen da suka dandana azabar ‘yansandan.

Rundunar ‘yan Sandan ta musanta zargin duk da yake tace ba’a rasa bara gurbi a kowanne sashe na al’umma.

You may also like