‘Yan Sandan Najeriya sun bace a kudancin kasar


 

Rahotanni daga yankin kudancin Najeriya na cewa, jami’an ‘yan sandan ruwa na kasar guda hudu sun bace bayan wani farmaki da ‘yan bindiga suka kai musu tare da sace jirgin ruwansu.

Wasu rahotanni sun ce, watakila ‘yan bindigan da ake zaton ‘yan fashin teku ne sun kashe jami’an ‘yan sandan.

An kai wa jami’an hari ne a lokacin da suke aikin sintiri a garin Abonnema da ke yammacin babban birnin jihar Rivers wato Fatakwal kamar yadda rundunar ‘yan sandan ta sanar a yau Laraba.

Kafafan yada labaran kasar sun rawaito cewa an kashe jami’an amma mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Nnamdi Omoni ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa, ya yi wuri a tabbatar da mutuwarsu.

Omoni ya ce, suna ci gaba da neman jami’an kuma kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki allhakin kai farmakin duk da dai ana zaton mayakan nan ne da ke fasa bututun man fetir na kasar.

You may also like