‘Yan Sandan Najeriya Sun Sanar Da Korar Wasu Jami’ai 3 Da Ke Kare Mawaki Dauda Kahutu RararaJami’an ‘yan sandan da bidiyonsu ya karade shafukan sada zumunta, an gansu suna harba bindigogi da harsasan gaske a sama, yayin da suke wa mawakin rakiya.

Al’amarin wanda ya faru a kauyen Kahutu garin mawakin, a ranar 7 ga wannan watan na Afrilu ya janyo Allah wadai daga jama’a daga sassa dabam-daban a kasar.

Dauda Kahutu Rarara (Instagram/Kannywoodcelebrties)

Dauda Kahutu Rarara (Instagram/Kannywoodcelebrties)

Wannan ya sa rundunar ‘yan sandan ta kamo jami’an tare da kaddamar da bincike kan al’amarin, abinda ya sa bayan binciken aka same su da laifukan yin amfani da makami ba bisa ka’ida ba, da wasa da aiki, da rashin da’a, da kuma yin hasarar harsasai.

Jami’an da aka samu da laifin, wato Sufeta Dahiru Shayibu, Saja Abdulkshi Badamasi, da Saja Isa Danladi daga bisani an koresu daga aiki.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like