‘Yan sandan Pakistan sun tarwatsa magoya bayan Imran Khan – DW – 02/11/2024‘Yan sandan Pakistan sun tarwatsa magoya bayan tsohon firaministan kasar Imran Khan da ke zanga-zanga a harabobin ofisoshin hukumar zaben kasar da ke birane daban-daban, ta hanyar harba musu hayaki mai sa hawaye.

Karin bayani:Ana gudanar da zabe a kasar Pakistan

Daga cikin garuruwan da aka gudanar da zanga-zangar har da Rawalpindi da birnin Lahore da sauran birane, inda suka rinka yin taho mu gama da ‘yan sanda babu kakkautawa.

Karin bayani:Burtaniya ta nuna damuwa game da tashe-tashen hankulan da ke faruwa a Pakistan

Yayin wani taron manema labarai da shugaban jam’iyyar PTI, Gohar Ali Khan ta tsohon firaminista Imran Khan, ya gudanar a Asabar din nan, ya bukaci magoya bayan na su su fantsama kan tituna, don nuna fushinsu da yunkurin da hukumar zaben kasar ke yi na magudin sakamako, bayan wadanda suka tsayar sun samu gagarumar nasara.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like