Yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane biyar a jihar Nassarawa


Rundunar yan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da mutuwar mutane biyar a wani sabon hari da aka kai kan kauyen Kadarko da kewayensa a karamar hukumar Obi ta jihar, a ranar Talata.

Kennedy Idrisu, mai magana da yawun rundunar, ya fadawa kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN,ranar Laraba a Lafiya cewa maharan sun dira kauyen da daddare inda suka shiga harbin duk mutumin da suka yi ido guda da ya da shi.

Ya ce rundunar ta tura isassun jami’ai domin kawo karshen harin ya kuma kara da cewa tuni aka samu kwarya-kwaryar zaman lafiya a yankin.

Ya ce rundunar ta kama mutane uku da ake zargin suna da hannu a harin na Kadarko.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like