‘Yan Shi’a Sun Bada Hadin kai Ga Kwamitin Binciken Rikicinsu Da Sojoji 


Kungiyar Shi’a ta bayar da hadin kai ga kwamitin da gwamnati ta kafa don binciken arangamar da  mabiya kungiyar suka yi da sojoji a shekarar 2015  wanda ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan Shi’a da dama.

Rahotanni sun tabbatar da cewa tunii kungiyar  ta Shi’a ta gabatar da bayananta ga kwamitin binciken. A cikin wata sanarwa, kungiyar ta nuna cewa Shugaban Kungiyar na Kasa, Malam Ibrahim El Zakzaky ne ya bayar da umarnin bayar da hadin kai ga kwamitin bincike bayan da ya sadu da lauyoyinsa a karo na biyu tun bayan da aka cafke shi.

You may also like