‘Yan Shi’a Sun Gudanar Da Zanga-Zanga A Ofishin Hukumar Kare Hakkin Dan AdamDaruruwan mabiya akidar Shi’a ne suka yi dandazo a hedkwatar hukumar kare hakkin dan Adam ta kasa ( NHRC) da ke Abuja a yayin da suke nuna adawa ga ci gaba da tsare Shugabansu na Kasa, Malam Ibrahim El Zakzaky.
Jagoran masu tarzoman, Abdullahi Musa ya nemi hukumar ta NHRC da ta sanya baki wajen ganin gwamnatin tarayya ta mutunta hukuncin kotun tarayya wadda ta umarci gwamnatin da ta gaggauta Sakin El Zakzaky cikin awanni 45 tare da biyansa diyya ta Naira milyan 50.
Shugaban Hukumar ta NHRC, Dr Oti Ovrawah ya yabawa ‘yan kungiyar kan yadda suka gudanar da tarzoman cikin lumana inda ya yi alkawarin tuntubar hukumomin da abin ya shafa don ganin an sako El Zakzaky.

You may also like