Yan Shi’a sun kona tutar Amurka da Isra’ila a Abuja


Wasu daga cikin ya’yan kungiyar yan uwa Musulmi da aka fi sani da Shi’a sun gudanar da zanga-zanga inda suka kona tutar kasar Amurka da kuma ta Isra’ila a birnin tarayya Abuja ihakan ya jawo zaman d’ar-d’ar a birnin.

Suna tafiya tare da rera wakoki da kada tuta mabiya akidar ta shi’a sun ce suna zanga-zanga ne kan yan kungiyar da aka kashe a yankin Falasɗinu.

Zanga-zangar ta fara ne daga babban masallacin Abuja ya zuwa shatale-talen Julius Berger dake birnin.

Yan sanda dauke da makamai sun ja tunga a wasu muhimman wurare domin hana karyewar doka da oda.

Masu zanga-zangar na dauke da allunan dake allawadai da kasar Amurka da kuma neman a saki Zakzaky da kuma samawa da kasar Falasɗinu yanci.

Daga bisani mutanen sun tattara karkashin gada inda suka kona tutar kasar Amurka da ta Isra’ila.

Zanga-zanga ta haifar da tsaiko ga zirga-zirga ababen hawa dama ta mutane akan hanyar kasuwar Wuse dake birnin.

You may also like