‘Yan Shi’a Sun Kwaci Bindiga Daga hannun ‘ Yan sanda Suka Bude Wuta – ASP Majiya Kano


An kashe Sajan din dan sanda tare da jikkata DSP a yayin artabun Shi’a da ‘yan sandan jihar Kano. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano DSP Magaji Musa Majiya, ya bayyana cewa, an kama ‘yan Shi’a 10 da zargin tayar da hatsaniyar. Majiya ya ce wani dan Shi’a ya kwaci bindiga AK47 daga wajen Sajan na dan sandan kwantar da tarzoma ya harbe shi sannan daga bisani suka gudu da bindigar. 

“‘Yan Sanda sun yi musu kawanya ne a yayin artabun, sai suka fara musayar wuta da ‘yan sanda. Wanda hakan ya janyo asarar ran dan Shi’a daya. Amma a karshe mun kwato bindigar daga wajen su. Majiya ya kara da cewa, daga baya Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano Alhaji Rabi’u Yusuf zai yi karin haske daga baya.

You may also like