Yan shi’a sun sake arangama da jami’an yan’sanda a Abuja


Ya’yan kungiyar yan uwa musulmi ta Najeriya da akafi sani da Shi’a sun sake arangama da jami’an tsaro a birnin tarayya Abuja.

Jami’an tsaro sun tarwatsa ya’yan kungiyar ranar Laraba yayin da suke  zanga-zangar neman a saki shugabansu Sheikh Ibrahim Elzakzaky wanda ake  cigaba da tsare da shi.

Yayan kungiyar, sun taru yanki na 10 dake unguwar Garki inda daganan suka yi jerin gwano zuwa yanki na 2 kafin daga bisani yan’sanda su dirar musu.

Yinkurin tarwatsa su yaci tura kafin daga bisani yan’sanda su shiga harbin iska.

Haka kuma jami’an tsaron sun yi amfani da barkonon tsohuwa abinda ya kawo rudani a yankin.

Sai dai wasu rahotanni na cewa mutane da dama sun jikkata a rangamar.

A ranar Litinin sai da jami’an tsaro suka hana ya’yan kungiyar shiga harabar majalisar ƙasa.

You may also like