Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta sun kashe yan ta’adda 20 suka kuma kama wasu 17 a yaƙin da suke da ƴaƴan ƙungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabas.
Mataimakin daraktan yaɗa labarai na runduna ta 8, Timothy Antigha a wata sanarwa da ya fitar yace mako biyu kenan rundunar ta shafe tana kai wani samame na musamman kan yayan kungiyar ta Boko Haram.
Yace maza magidanta 100, mata da kuma ƙananan yara da ake tsare dasu ba tare da son ransu bane aka samu nasarar cetowa.
“A ci-gaba da samamen da ake kira “Operation Deep Punch” a turance, wanda aka tsara domin fatattakar yan kungiyar Boko Haram dake rayuwa a wasu tsibirai dake tafkin Chadi bangaren dake cikin Najeriya, sojojin runduna ta 8 na sojin Najeriya dake aiki a shirin samar da tsaro na “Operation Lafiya Dole” da taimakon wasu sojojin sun yi wa yayan kungiyar Boko Haram gagarumar ɓarna.” sanarwar tace.
“Samamen da aka fara makonni biyu da suka wuce an yi shine bayan da aka yi ruwan wuta ta sama da kuma bindigogin atilare akan wasu tsibirai da yan ta’addar suka mamaye inda daga nan suke shiga cikin Magumeri, Kauram da sauran wurare su aikata yan sace-sace sannan kuma su kaiwa jami’an tsaro hari da kuma wasu ƙauyuka garuruwan da aka kori yan ta’addar sun haɗa da Chiki, Chikun Gudu, Arena Waje, Sa’ada da Juwe da sauran su.
“Yan ta’adda 20 aka kashe aka kuma samu nasarar kama 17 yayin da aka ceto mutane 100 da suka haɗa da maza mata da kuma ƙananan yara.Binciken farko da rundunar ta yi ya gano cewa yawancin mutanen da aka ceto an tsare su ne ba tare da son ransu ba inda ake tilasta musu aiki a gonaki cikin wani yanayi mai muni gaske.”
Rundunar ta cigaba da cewa ya zuwa yanzu babu jami’in ta kwaya daya da ya rasa ransa a samamen, sai dai sojoji 6 ne suka samu raunuka kuma suke can suna karɓar magani.
An dai gano makamai da dama da suka haɗa da bindigar kakkabo jiragen sama, motocin hawa da sauransu.