‘Yan ta’adda Da Dama Sun Halaka A Kasar Syria


 

Sojojin Kasar Syria Sun Kashe ‘Ya ta’adda Da Dama A yammacin Kasar

Kamfanin Dillancin Labarun ( Sana) na kasar Syria ya ambato cewa; A  yau alhamis sojojin kasar sun yi fada da kungiyoyin ‘yan ta’addar Jubhatun-Nusrah, da Ahrarus-sham a yankin Humah da ke yammacin kasar, tare da kashe da dama daga cikinsu.

Bugu da kari, sojojin kasar ta Syria sun dakile kokarin ‘yan ta’addar na kutsawa cikin irnin na Hamah, ta hanyar dasa bama-bamai da wasu abubuwa masu fashewa.

A garin Zakiyah, sojojin Syria sun killace sansanin ‘yan gudun hijira na Khan Sheikh da zummar kwace shi daga hannun ‘yan ta’adda.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like