‘Yan Ta’adda Sun Kai Hari Masallacin Dan Fodio Dake Garin JalingoA Daren Jiya Misalin Karfe 2:30 Zuwa Karfe 03:00  Wasu Yan Ta’adda Dauke Da Makamai Suka Kai Hari A Masallacin Uthman Bin Fodiyo Dake Garin Jalingo (Izala Central Mosque). Wanda Akafi Sani da Masallacin Dr. Ibrahim Jalo Muhammad.
Mai Gadin Masallacin (Baba Dan Alhaji) Ya Shaida Cewa Yana Cikin Aiki Sai Ya ga Wani Mutum Ya Shigo Cikin Masallacin. Da ya tinkare shi Sai Ya ga Muggan Makamai A Hanunshi. Sai Dan Ta’addan Yace Mishi Kana Daga Cikin Shugabanin Masallacin Nan Ne. 
Sai Baba Dan Alhaji yace mishi Shi Mai kula da Masallacin Ne. Nan Take Mai Gadin Ya Bar shi Ya koma Dayan Bangaren Masallacin. Sai Ya fara Kiran Waya Domin A Kawo Mishi Dauki.
A Lokacin ‘Yan Ta’addan Sun Fara Fasa Gilasan Windon Masallacin.
Sai Wani Daga Cikin Masu Gadin Shaguna Dake Yamma Da Masallacin Ya Ji Karar Fasa Gilas. Sai Ya Leko Cikin Masallacin Ya Kuma Kira Mai Gadin Gidan Man A.A. Rano Da Wasu ‘Yan Banga.
Suka Nufo Cikin Masallacin Sai Sukaga Biyu Daga Cikin Yan Ta’addan Sun Tsallake Katanga Da Bindiga A Hanunsu. Da Suka ga Haka. Sai Suka Haska Wa Dayan Dake Cikin Masallacin Toci A Ido. Sai Sukaga Ya Warware Bindigar Sa. Cikin Taimakon Allah Suka Afka Mishi Suka Kama shi Da Duka.
Daga Nan ‘Yan Banga Suka Wuce Dashi Ofishin Su. Yanzu haka An Mikashi Ga Jami’an Tsaro.

You may also like