Yan Ta’adda Sunyi Sanadiyyar Rayuka 34 A Sabon Harin Da Suka Kai A Zamfara


Akalla mutane 34 suka rasa rayukansu sakamakon wani mummunan hari da wasu ‘yan ta’adda suka kai a kauyakun Kabaro, Danmanin Hausawa da Danmanin Dakarkari da ke cikin karamar hukumar Maru a jihar Zamfara.

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan ta’addan wadanda ake zargin Makiyaya ne sun kai farmakin ne a kan babura kuma ana ganin harin fansa ce a kan cafke masu mutane biyar da sojoji suka yi kwanaki. Sarkin Dansadau, Alhaji Husaini Umar ne dai ya jagoranci Sallar jana’izar wadanda suka rasa rayukansu.

You may also like