Yan Ta’addan Da’ish A Iraki Suna Amfani Da Fararen Hula A Matsayin Garkuwa A Garin Mosel


4bka51f781c139gh2v_800c450

 

‘Yan kungiyar ta’addanci ta Da’ish a garin Mosel na kasar Iraki suna amfani da fararen hula a matsayin garkuwa da nufin kawo cikas ga shirin sojojin kasar na yantar da garin daga mamayar ‘yan ta’adda.

A ganawarsu da manema labarai bayan kubuta daga kangin ‘yan ta’adda a garin Mosel: Al’ummar garin na Mosel suna kokawa kan yadda ‘yan ta’addan kungiyar Da’ish suke yin garkuwa da mutane da nufin zame musu katanga tsakaninsu da sojojin Iraki da suke ci gaba da samun nasarar ‘yantar da yankunan garin.

Har ila yau al’ummar garin na Mosel suna kokawa kan yadda ‘yan ta’addan kungiyar ta Da’ish suke kashe mutanen da suka kama a kan hanyarsu ta kokarin ficewa daga garin.

You may also like