Yan Tawaye A Kasar Afrika Ta Tsakiya Sun Fara Kisan Kabilar Fulani A Kasar


4bkbfb2dd69a10i61a_800c450

 

Wata kungiyar yan tawaye a kasar Afrika ta Tsakiya tana kiyar yan kabilar Fulani a kasar tun ranar litinin da ta gabata.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto Jami’i mai bada shawara na musamman kan kisan kare dangi na majalisar dinkin duniya yana fadar haka a jiya jumma’a.

Adama Diaring ya kuma kara da cewa mayakan kungiyar Popular Front for the Renaissance of Central African Republic (FPRC) suna zakulo yan kabilar Fulani kadai daga cikin kungiyar the Union for Peace in Central Africa (UPC) a garin Bria kilomita kimani 600 daga birnin Bangui babban birnin kasar suna kashewa.

Rahoton ya kara da cewa yan tawayen na FPRC sun shiga cikin garin Bria da kuma Bambari suna shiga gida suna zakulo yayayn wannan kabilar suka kashewa, irin kisan da yana iya shiga karkashin kisan kiyashi ko kisan kare dangi wanda ake iya sauraron kararsa a kutunan kasa da kasa.

Ya zuwa yansu dai mutane a kalla 85 suka kashe kuma wasu 76 suka je rauni amma yayan kungiyar ta FPRC suna zuwa asbotoci don hana janyan duk dan kabilar Fulani da aka kawo.

Dukkanim kumgiyoyin biyu sun kasance cikin kungiyar Seleka wacce ta kifar da gwamnatin Fransua Bozize a shekara ta 2013 amma daga baya ta tarwatse.

You may also like