‘Yan tawaye Kwalambiya za su zama jam’iyya


 

 

Kungiyar Tawayen FARC a Kwalambiya ta bude taron na canza sheka zuwa kafa jam’iyyar siyasa.

019559310_30300

A Kwalambiya Kungiyar ‘yan tawayen Farc mai akidar Makisanci ta bude babban zaman taron congres dinta karo na 10 a wannan Asabar a birnin El Diamante na Kudu maso Gabashin kasar domin samun matsaya game da batun kawo karshen tawaye da kuma saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin kasar.

Wakilai kimanin 500 a karkashin jagorancin madugun ‘yan tawayen Kungiyar ta Farc Rodrigo Londono da aka fi sani da sunan Timochenko suke halartar babban taron Kungiyar wanda aka bayyana a matsayin wanda zai tsaida sabuwar alkiblar makomar kasar ta Kwalambiya, bayan da aka share shekaru 52 ana gobza fada tsakanin gwamnati da ‘yan tawayen na Farc ba tare da wani ya samu nasara kan abokin gabarsa ba.

Kazalika taron wanda za a share kwanaki takwas ana gudanar da shi zai kuma tattauna batun rikidewar kungiyar tawayen ta Farc zuwa jam’iyyar siyasa.

You may also like