‘Yan tawaye sun kori dakarun Syria a Aleppo


 

2016-08-06t181500z_2075474977_s1bettxqrcaa_rtrmadp_3_mideast-crisis-syria-breakthrough

Gwamnatin Syria ta sake tura dakarunta zuwa yankin Aleppo bayan ‘Yan tawaye sun sanar da karya lagon dakarun a yankin da suka yi wa kawanya. Dakarun na Syria dai na tsoron mamaya ne daga ‘Yan tawayen a yankin da suke iko a Aleppo.

Rahotanni sun ce ‘Yan tawayen sun kori dakarun na Gwamnatin Bashar al Assad daga yankin na Aleppo, domin bude hanya ga mutanen yankin na gabashi masu makwabtaka da Aleppo da aka mamaye.

Yanzu dai murna ta barke tsakanin mutanen yankin sama da dubu dari da ashirin da biyar da ke bukatar agaji.

You may also like