‘Yan tawaye sun kwace sansanin sojoji a Mali


 

Wasu da ake zargi masu jihadi cikin motoci da babura sun kai hari a wani sansanin sojoji da ke tsakiyar Mali wato a garin Nampala, inda suka karbe iko da yankin.

Wasu da ake zargi masu jihadi, sun kai hari a wani sansanin sojoji da ke tsakiyar kasar Mali a birnin Nampala. A cewar magajin wani gari da ke kusa da yankin ya ce “Mayakan sun zo da manyan motoci hudu wasu kuma a kan babura, amma dakarun gwamnatin na sake jan damara a birnin Diabaly dan kwace iko da sansanin.”

Kimanin sojoji 10 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikata a harin. A shekara ta 2013, kasar Faransa ta jibge dakarunta a kasar Mali da nufin fatattakan mayakan da ke yunkurin mamaye arewacin Mali. Ko a kwanan ma an rattaba hannu kan yarjejeniya da wasu ‘yan tawayen Mali a Jamhuriyar Nijar da nufin ajiye makamai dan kwantar da tarzoma.

You may also like