A Nigeria, mayakan ‘yanto ‘yancin yankin Niger Delta wato Niger Delta Avengers sunce yau Asabar sun kai wani kazamin hari a yankin na su, wanda shine irinsa na farko tun bayan yarjejeniyar tsagaita wuta don yin sulhu da suka kulla da mahukuntan kasar a watan jiya.
‘Yan Tsagerun sun bayyana cewa sun tarwatsa bututun mai a yankin Bonny, daren jiya Juma’a, wanda yake da muhimmanci wajen samawa kasar kudaden shiga.
Sanar tasu ta yanar gizo na cewa burin su ya cika don sun lalata aikin hakar man fetur a yankin na Bonny.