‘Yan Wasa Da Magoya Bayansu 30 Sun Nutse A Teku A Kasar Uganda


 

4bkc1b4804803ek47p_800c450

 

Alal akalla ‘yan wasan kungiyar kwallo da magoyo bayansu su 30 ne suka nutse a lokacin da wani karamin jirgin ruwan da ke dauke da su ya kife a tafkin Alberta da ke kudancin kasar Uganda.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya jiyo wani kwamandan ‘yan sandan kasar Ugandan John Rutagira yana tabbtar da wannan labarin inda ya ce ‘yan wasan kwallon kafan da magoya bayan na su sun taso ne daga kauyen Kaweibanda da ke lardin Bullisa a hanyarsu ta zuwa gundumar Hoima don buga wani wasa na sada zumunci.

Mr. John Rutagira ya kara da cewa mutanen da ke cikin karamin jirgin sun kai 45 wanda hakan ya  dara adadin mutanen da jirgin yake dauka, sannan kuma suna ta tsalle-tsalle sakamakon giyar da suka sha don haka jirgin ya kife. Jami’in ‘yan sandan ya ce alal akalla  mutane 30 daga cikin mutanen da suke cikin jirgin sun mutu.

Shi dai Lake Albert din yana kan iyakan kasashen Uganda da Demoradiyyar Kongo ne kuma an sha samun irin wannan hatsarin a cikinsa.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like