‘Yan Wasan Black Stars Sun Yi Wa Marigayi Christian Atsu Karramawar Karshe
‘Yan wasan Black Stars na kasar Ghana sun hallara a birnin Kumasi don shirye shiryen da suke yi na wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika da zasu yi da Angola ranar Alhamis.

A karshen horon nasu na ranar Talata ne suka hadu suka kai gaisuwar bankwana ga dan wasan, wanda aka yi taron jana’izarsa ranar 17 ga wannan watan Maris. Girgizar kasa mai karfin maki 7.8 da ta faru a kasar Turkiyya da Syria kwanan baya ce ta yi sanadiyyar mutuwar Atsu a ranar 6 ga watan Fabrairu a Turkiyya.

Tsohon dan wasan na Chelsea da New Castle United dai an tabatar da mutuwarsa ne kwana 12 bayan faruwar girgizar kasar, bayan da aka gano gawarsa a cikin baraguzan gine-gine. Atsu dai ya yi wa Black Stars wassani 65 inda ya zura kwallaye tara.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like