
Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid za ta karbi bakuncin Elche a wasan mako na 21 a La Liga da za su kara a Santiago Bernabeu ranar Laraba.
Ranar 19 ga watan Oktoban 2022, Real ta je ta ci Elche 3-0 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Real Madrid tana ta biyu a teburi La Liga da tazarar maki 11 tsakaninta da Barcelona mai jan ragama mai maki 56.
Elche wadda take da maki tara tana ta karshen teburin La Liga ta 20 kenan.
Ranar Asabar Real ta lashe World Club Cup, bayan cin Al Hilal 5-3 a Morocco.
Tuni Carlo Ancelotti ya bayyana ‘yan wasan da zai fuskanci Elche
Masu tsaron raga: Lunin, Luis López da kuma Cañizares.
Masu tsaron baya: Carvajal, Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Odriozola, Lucas V. da kuma Rüdiger.
Masu buga tsakiya: Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni, D. Ceballos da kuma Arribas.
Masu cin kwallaye: Benzema, Asensio, Rodrygo da kuma Mariano.