
Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid za ta karbi bakuncin Villareal a wasan mako na 28 ranar Asabar a Santiago Bernabeu.
Kungiyoyin sun fafata sau biyu a bana, inda Real ta fitar da Villareal a Copa da Rey, amma aka doke ta 2-1 a La Liga.
Wasa biyu da aka buga Real da Villareal a bana
Copa del Rey Alhamis 18 ga watan Janairu
- Villarreal 2 – 3 Real Madrid
La Liga Asabar 7 ga watan Janairun 2023
- Villarreal 2 – 1 Real Madrid
Real za ta buga wasan da kwarin gwiwa, bayan da ta doke Barcelona 4-0 a Copa del Rey ranar Laraba a Nou Camp.
Kenan Real ta kai wasan karshe a Copa del Rey za ta fafata da Osasuna kenan.
Barcelona ce ta daya a kan teburin La Liga da maki 71, Real Madrid ce ta biyu mai maki 59 da tazarar maki 12 tsakaninta da kungiyar Nou Camp.
Atletico Madrid mai maki 54 tana ta uku, ita kuwa Villareal tana mataki na shida a teburin La Liga mai maki 44.
Masu tsaron raga: Courtois, Lunin, Luis Lopez.
Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Odriozola, Lucas V., Rüdiger.
Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni, D. Ceballos.
Masu cin kwallaye: Hazard, Benzema, Asensio, Vini Jr., Rodrygo, Mariano.
Wasannin mako na 28 da za a buga:
Juma’a 7 ga watan Afirilu
Asabar 8 ga watan Afirilu
- Osasuna da Elche
- Espanyol da Athletic Bilbao
- Real Sociedad da Getafe
- Real Madrid da Villarreal
Lahadi 9 ga watan Afirilu
- Real Valladolid da Real Mallorca
- Real Betis da Cadiz
- Almeria da Valencia
- Rayo Vallecano da Atletico Madrid
- Barcelona da Girona