Yanayin ‘Yan Gudun Hijira Na Ci Gaba Da Tabarbarewa A Afirka Ta Tsakiya


 

Kungiyoyin farar hula na ciki da wajen jamhuriyar Afirka ta tsakiya, sun yi gargadi dangane da halin da ‘yan gudun hijira suke ciki a kasar, sakamakon matsalolin tsaro da kuma karancin abubuwan bukatar rayuwa.

A cikin wani bayani na hadin gwiwa da kungiyoyin suka fitar, sun bayyana yanayin da ake ciki da cewa yana ban tsoro matuka, domin kuwa ‘yan gudun hijira suna cikin mawuyacin hali na karancin abubuwan bukatar rayuwa, wanda majalisar dinkin duniya da sauran kasashen duniya ba su yunkura da wuri ba, akwai yiwuwar hakan ya haifar da gagarumar matsala a sansanonin da suke.

Haka nan kuma bayanin ya kara da cewa matsalar rashin tsaro ta sake dawowa a yankuna daban-daban na kasar, inda kungiyoyin Anti balaka da kuam Seleka dukkaninsu suke kai hare-hare kan junasu da kuma jama’ar gari, wanda dakatar da hakn na bukatr sa hannun kasashen duniya.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like