An Yankewa Wata Mata Hukuncin Shekaru 90 a Gidan Yari a Bisa Laifin Danfarar Dalibai


chika-amsy-charles-3-e1477658034999

 

Wata kotu a jahar Enugu ta yankewa wata mata hukuncin daurin shekaru 90 a gidan kasu a bisa laifin danfarar wasu matasa masu neman shiga jami’a.

Hukumar EFCC ita ta gurfanar da matar mai suna Chika Amsy Charles a gaban kuliya,  inda ta tuhume ta da laifuka har guda 30.

Hukuncin shekaru 90 din ya kunshi na shekaru uku uku akan kowanne laifi daya da aka kama matar da shi, kuma za ta fuskanci hukuncin ne a jere.

Chika dai ta danfari wasu matasa guda 3 zunzurutun kudade har Naira miliyan 5.6 da nufin za ta taimaka masu su a dauke su a jami’ar Kimiyya da Fasaha ta jahar Enugu.

Ta iya yin hakan ne ta hanyar wata kungiya mai zaman kanta da ta kafa mai suna ‘Bold and Dynamic Gender Initiative’ wanda ko rajista ba ta yi mata ba.

Dubun ta ya cika a shekarar 2007 a lokacin da daya daga cikin matasan da ta danfara ya rubuta takardar korafi zuwa hukumar EFCC, wacce ta kama ta sannan ta gurfanar da ita a gaban kuliya.

You may also like