Yan’sanda a Gombe sun kama mutanen da suka yi garkuwa da wani ma’aikacin jiya 


Rundunar yan’sanda ta jihar Gombe ta ce ta kama wasu mutane huɗu da ake zargi da yin garkuwa da wani ma’aikacin jiya dake aiki da gwamnatin jihar, watanni biyu da suka wuce.

Mista Ephraim Ajuji, sakataren wani karamin asibiti dake garin Hina a Karamar Hukumar Yamaltu-Deba ta jihar, wasu yan bindiga ne da ba a san ko su waye ba su kayi garkuwa da shi da safiyar ranar 31 ga watan Oktoba.

Da yake gabatarwa da manema labarai mutanen da ake zargi ranar Litinin a hadikwatar yan’sanda ta jihar, kwamishinan yan’sandan jihar, Shina Tairu Olukola ya ce runduna ta musamman dake  yaki da fashi da makami wacce akafi sani da SARS ce ta samu nasarar kama mutanen.

Ya ce mutanen da ake zargin sun haɗa da Muazu Adamu da akafi sani da Dabo mai shekaru 27 dan asalin karamar hukumar Alkalere ta jihar Bauchi, Bodori Maifada dan asalin karamar hukumar Balanga, da kuma Wada Adamu mai shekaru 26 dan asalin ƙaramar hukumar Yamaltu-Deba dukansu su amince da kasancewa cikin gungun wasu bata gari da suka sace ma’aikacin jiyar.

Olukola ya ce mutanen da ake zargi suna cigaba da taimakawa yan’sanda da bayanai da za su kai ga kama sauran mutane uku da har yanzu ake nema ruwa a jallo.

Kwamishinan ya ce bindiga kirar AK-47 da kuma kuɗi ₦200,000 na daga cikin kayayyakin da aka gano a hannun mutanen.

You may also like