Yansanda a birnin Abidjan na kasar Ivory Coast sun tarwatsa taron yan adawa wadanda suke nuna rashin amincewarsu da sauya kundin tsarin mulkin kasar.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa yansandan sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa taron a safiyar yau Alhamsi sun kuma kama wasu fitattun yan adawa da kuma magoya bayan tsohon shugaban kasar Lauranta Bagbo kimani 20.
Wani jigo a cikin yan adawan da aka kama mai suna Mamadou Koulibaly ya fadawa reuters cewa sun fito ne don nuna rashin amincewarsu da sabon kundin ts
arin mulkin kasar kamar yadda tsarin Democradia ta bukata amma ga Alhasan Watara nan yana jafamu cikin kurkuku, don haka a gayama bazamu fasaba.
Shugaban kasar ta Ivory Coast Alhasan Watara ya bayyana cewa sabon kundin tsarin mulkin kasar zai kawo karshen matsalolin kabilanci da bangarenci wadanda kasar tayi ta fama da su a shekarun bayan. A karshen wannan wata ne ake saran mutanen kasar Zasu gudanar da zaben raba gardama kan sabon kundin tsarin mulkin kasar, wanda aka ciccire wasu dokoki wadanda suke hana wanda iyayensa biyu duka ba yan kasarba rike mukamin shugaban kasa.