Yan’sanda sun kama Fulani makiyaya 8 a jihar Benue


Yan’sandaa a jihar Benue sunce suna tsare da Fulani makiyaya  8 game da mutuwar mutane goma a ƙaramar hukumar Goma da Logo dake jihar.

Moses Yamu, jami’in hulda da manema labarai na rundunar shine ya sanar da haka cikin wata sanarwa da yafitar  ranar Laraba.

“Makiyaya  shida a Guma biyu kuma  a Logo aka kama  da ake zargi da hannu a kisan,”mai magana da yawun rundunar yace.
 Ya kara da cewa rundunar ta ƙara tura karin jami’an tsaro domin hana faruwar haka anan gaba da kuma da dawowa jama’a kwarin gwiwa.

Yamu, yace an shawo kan matsalolin dake faruwa a kananan hukumomin biyu yayin da ake cigaba da bincike.

A ranar Talata, gwamnan jihar Samuel Ortom yace mutane 20 aka kashe a hare-haren.

Dokar jihar Benue ta hana kiwo a fili ta fara aiki ne ranar 1 ga watan Nuwambar shekarar 2017 domin kawo karshen  harin da ake zargin Fulani makiyaya da kaiwa kan al’ummomi dake jihar.

Harin shine na farko da ake zargin Fulani da kaiwa tun bayan da dokar ta fara aiki.

You may also like