Yan’sanda sun kama mutane biyu da ake zargi da yin garkuwa da kuma kashe wani mutum a jihar Zamfara


Rundunar yan’sanda a jihar Zamfara ta kama mutane biyu(wadanda aka boye sunansu) da ake zargi da hannu wajen  yin garkuwa da kuma kisan  wani mutum  mai suna Sani Sa’idu, dake kauyen  Guru a karamar hukumar Maru.

A wata sanarwa da rundunar ta fitar ranar Laraba a Gusau, mai magana da yawun rundunar, DSP Muhammad Shehu, yace mutanen da ake zargi an kama sune ranar Talata a garin Dansadau dake karamar hukumar ta Maru.

Shehu ya ce an kama masu laifin ne yayin wani samame a dajin da suke boye a yankin.

Yace mutanen da ake zargin sun fito ne daga kauyen  Malele dake yankin Dansadau na ƙaramar hukumar.

Yace mutanen da ake zargi a ranar 26 ga watan Nuwamba sun yi garkuwa da Sa’idu dan asalin kauyen Guru na ƙaramar hukumar Maru inda suka halaka shi daga baya.

Mai magana da yawun rundunar yan’sandan yace an gano bindiga guda ɗaya kirar gida da kuma babur na hawa a a gurin mutanen.

Ya kara da cewa za gurfanar da mutanen a gaban kotu da zarar rundunar ta kammala bincike.

You may also like