Yan’sanda a jihar Borno sun kama wani mutum mai suna, Gaji Adamu da ake zargi da laifin kashe wasu yara biyu daliban wata makarantar firamare a karamar hukumar Kwaya-Kusar dake jihar.
Mai magana da yawun rundunar yan’sandan jihar, Victor Isuku shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da yafitar ranar Alhamis a Maiduguri.
Isuku yace lamarin yafaru da misalin ƙarfe 9:30 na safe, a ranar Alhamis lokacin da mutumin da ake zargi ɗauke da adda ya kai hari kan yara ƴan makarantar firamare ta Jafi.
Ya kara da cewa mutumin ya kashe ɗalibai biyu maza tare da raunata wata Malama da kuma daliba mace guda ɗaya.
Mai laifin wanda ake zargin yana da cutar tabin hankali ya gamu da fushin matasa inda suka lakada masa dukan kawo wuka.
Mai magana da yawun rundunar yan’sandan yace gawarwakin yaran da kuma wadanda suka jikkata an tura su babban asibitin Gombe,dake jihar Gombe mai makotaka da jihar yayin da aka tsare mutumin da ake zargi da aikata laifin a asibiti karkashin kulawar yan’sanda.
Kwamishinan yan’sandan jihar Damian Chuku ya bada umarnin a mayar da bincike kan laifin zuwa sashen binciken manyan laifuka na rundunar domin su cigaba da bincike da kuma tantance gaskiyar cutar tabin hankali da yake fama da ita.