Rundunar yan’sandan jihar Kaduna ta tabbatar da kama wani mutum da ake zargi da hannu ayin garkuwa da wani shugaban matasa, Malam Bashir Ahmad.
Mai magana da yawun rundunar yan’sanda ta jihar, Mukhtar Aliyu shine ya tabbatar da kamen jiya a Kaduna.
An yi awon gaba da Malam Bashir a yankin Tudunwada dake birnin Kaduna.
Wani sheda da ya ganewa idonsa abinda ya faru yace wasu yan bindiga da suka rufe fuskokinsu ne suka yi awon gaba da Malam Bashir.
Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta Tsakiya,Shehu Sani ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa: ” Yanzu na samu labarin sace daya daga cikin shugaban matasa na kuma ɗan uwana Mallam Bashir Ahmad da wasu yan bindiga suka yi a yankin Tudunwada dake yankin Kaduna ta Kudu.”