‘Yansanda a jIhar Borno a yau lahadi sun tabbatar da mutuwar ‘yan kunar bakin wake maza 2 a Maiduguri.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandar jihar Mr Victor Isuku a jawabinsa a Maiduguri yace harin farko ya farune a garejin Muna dake kusada ƙofar shigowa garin inda maza ‘yan ƙunar bakin wake biyu suka rasa rayukansu.
” A yau misalin 4:38, mutane ‘yan kunar bakin wake suka sa bam a jikinsu kusa da garejin Alhaji Bukar Gujari dake Muna a ƙofar shigowa gari.”
Isuku yace duk ‘yan ƙunar bakin waken sun mutu ,yace bam din yayi fata-fata da motar da aka aje kusa dasu.
Sannan Isuku ya ƙara da cewa bam yatashi a ƙauyen dasuna inda ya kashe mai sanye da bam ɗin sannan ya jiwa mutum 1 rauni.