Yansanda Sun Tarwatsa Taron Yan Shi A Gaban Majalisar Dokokin Kasar A Abuja


Shiites-protest1

 

Yansanda a birnin Abuja na tarayyar Nigeria sun tarwatsa taron yan shia mabiya Sheikh Ibrahim El-Zakzagi wadanda suke zanga zangar neman a saki malaminsu a kofar shiga majalisar dojojin kasar a jiya Laraba.

Shafin yanar gizo na saraha reporters ya bayyana cewa tun farko yansandan sun bukaci masu zanga zangar kada su shiga harabar majalisar dokokin kasar amma suka yi burus da bukatar, a nan ne yansandan suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye don tarwatsasu. Kuma yan shi’an sun maiyawa yan sandan gongonan hayakin da suke jefa masu.

Banda haka wasu daga cikinsu sun nuna turjiya a lokacinda yansandan suke kokarin kamasu.

Tun fiye da shekara guda ne jami’an hukumar DSS take tsare da sheikh Ibrahim El-Zakzagy da matarsa da wasu yayan kungiyar harka Islamiyya da dama. Kuma gwamnatin bata bi umurnin kotu na a sake shi a kuma biya shi diyya.

 

Shiites-protest7

 

 

 

 

 

Shiites-protest4

 

Shiites-protest5

 

 

 

 

 

Shiites-protest6

 

 

 

 

Shiites-protest12

 

 

 

 

Shiites-protest9

 

 

 

Shiites-protest1

 

 

 

 

 

You may also like