Hukumar yansandan ciki a tarayyar Nigeria ta bada sanarwan kame yan kungiyar Boko Haram akalla 13 a cikin sabuwar shekara da ta kama.
Jaridar Primium time ta Nigeria ta nakalto majiyar hukumar tana bayyana haka a jiya Talata ta kuma kara da cewa jami’an hukumar sun kai sumame a ranar 10 ga watan Jenerun da muke ciki wato a jiya kenan a yankin Oko Oba na jihar Lagos inda suka kama mutane 4 wadanda suke tuhuma kan cewa yayan kungiyar Boko Haram ne da suke tsare daga yankin arewa maso gabacin kasar zuwa birnin na Lagos.
Banda haka labarin ya kara da cewa sunayen wadanda abin ya shafa dai sun hada da Fanayi Bukar Hassan, Butame Hassan, Kologoni Bukar, da kuma Amina Abubakar.
Sai kuma Abdullahi Mohammed wanda jami’an hukumar suka kama a garin Okene na jihar Kogi inda suka tabbatar da cewa shi ne shugaban yayan wannan kungiyar a yankin.Sai kuma Muhammad Auwal wanda hukumar ta DSS suka kama a kauyen Andaza na karamar hukumar kiyawa a jihar Bauchi. Hukumar ta ce da alamun Muhammad Auwal yana aiki wa kungiyar ta Boko Haram a matsayin mai sayar masu magunguna.