Inna Ilaihi Wa Inna Ilaihi Rajiun
Allah Ya yi wa Limamin babban Masallancin Juma’a na Suleja, Sheik Muhammad Dantani rasuwa a safiyar yau.
Malam ya rasu ya bar mata uku da ‘ya’ya da kuma jikoki da dama inda za a yi jana’izarsa da misalin Karfe 11 na safiyar yau.
Allah Ya jikan Malam da gafara.