An samu tashin bamabomai guda biyu a garin Mubin jihar Adamawa da tsakiyar ranar yau Talata.
Ababen fashewan sun tashi ne a tsohuwar kasuwan Mubi (Kasuwan ‘Yan Gwanjo) kusa da masallaci.
Wani wanda yake kasuwan lokacin da abun ya faru ya shaida wa wakilin mu cewa Bom na farko ya tashi ne da misalin karfe 1:10pm. Yace na biyun kuma ya tashi mintuna kadan bayan jama’a sun fara taruwa a wurin da na farkon ya tashi.
Shu’aibu Saleh, mazauni a garin na Mubi ya shaida wa wakilin mu cewa an samu asaran rayuka sosai wanda kawo yanzu ba’a san adadin su ba.
Garin na Mubi dai ya sha fama da fitinar ‘yan Boko Haram wanda a shekarar 2014 suka kafa tuta a garin tare da sauya sunan zuwa Madinatul-Islam, kafin dakarun sojoji sukayi waje da su daga garin.