Yanzu-Yanzu: James Rodriguez Ya Koma Kungiyar Bayern Munich


Dan Wasan Tsakiya na Kungiyar Real Madrid ya koma kungiyar Bayern Munich a matsayin aro na tsawon shekara biyu. 

Zuwan sa zai bawa Douglas Costa damar zuwa Juventus, tunda Rahotanni sun nuna cewa Kungiyar ta Juventus ta dade tana zawarcin Douglas Costa. 

Kungiyoyi da dama sun dade suna neman dan wasan na real madrid dan kasar Columbia, kungiyoyi kamar su Manchester United da Chelsea sun dsde suna neman dan wasan daga karshe dai ya koma Bayern Munich. 

You may also like