‘Yar Kano ta auri baturen kasar Amurka


Wannan wata baiwar Allah ce daga jihar Kano wadda sukayi aure da wani baturen kasar Amurka, sun shafe shekaru biyu suna soyayya amma basu taba haduwa ba, bata boye mishi komai ba ta gayamai ta taba yin aure kuma tana da yaro.
Da yake Allah ya kaddaro matar mutum kabarinshi sai gashi baturen wanda ya karbi addinin musulunci kuma sunanshi Musa yazo har garin Kano aka daura musu aure a unguwar Birger, ranar talatar data gabata, an kuma yi walimar buda baki a Abuja.

Like it? Share with your friends!

0

You may also like