Yara 20 sun rasu cikin mako daya a hare-haren Siriya


589f0cca2dd10 (1)

 

 

Yara kimanin 20 ne suka rasu a mako guda a Siriya dukda anyi harjejeniyar tsagaita wuta.

Kungiyar UNICEF ta ce ya kamata abar duk wata tawaga ko kungiyoyin taimako su kaiwa yaran Siriya taimakon magani da sauran abubuwa.

Bisa ga bayanin da daraktan UNICEF Geert Cappelaere na Siriya ya yi, tsabar tsananin yanayin rayuwa a kasar Siriya yara 20 ne suka rasa rayukansu a mako guda, tare da jikkatar wasu da dama. Cappelaere ya cigaba da cewa “mutane 30 ne suka rasu wanda 16 cikinsu yara ne a garin Idlib a farkon makon da ya wuce. Wasu daga cikin wanda suka rasun sun rasa gidajensu a yakin birnin Aleppo, inda hakan ya sa su gudun hijira.”

Cappelaere ya kara da cewa yara 4 ne suka rasu yayinda 5 suka jikkata a harin da aka kai yankin Zehra da Vaer yayinda ya ce wannan na daya daga cikin manyan hari da aka yi tunda aka yi yarjejeniyar tsagaita wuta a 30 ga watan Disamba.

Cappelaere ya jaddada cewa ya kamata a dakatar da wadannan hare-hare cikin kankanin lokaci yayinda kara da cewa “Kashe yara ko kuma jikkatasu ya sabawa hakkin yara da aka kafa shekara da shekaru.”


Like it? Share with your friends!

0

You may also like