Yarabawa Na Kokarin Ganin Sun Mayar Da Osinbajo Shugaban Kasa inji Cewar Matasan ArewaGamayyar kungiyoyin matasan Arewa sun zargi Jagororin Yarabawa da kulla makarkashiyar kaddamar da Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin shugaban kasa. 

Gamayyar kungiyoyin sun fitar da wata sanarwa wacce Muhammed Shehu da Tanko Abdullahi suka rattabawa hannu, sun ce Jagororin Yarabawa na yunkurin yi wa Arewa kutungwila domin Osinbajo ya zama shugaban kasa. 

Taron da matasan suka yi a Daura, sun sha alwashin cewa, duk gumurzun da za a yi sai Arewa sun yi shekara takwas suna Mulki.

You may also like