Yarabawa Sun Kaddamar Da Ofishin Yaƙin Neman Zaɓen Buhari A 2019


A cigaba da shirye-shiryen yakin neman zaben 2019 mai zuwa, ministan sadarwa wato Adebayo Shittu dashi da takwaransa ministan lafiya wato Isaac Adewole da kuma tsohon shugaban Majalisar dattawa wato sanata Ken Nnamani da kuma tsohon gwaunan jahar Abia wato Orji Uzor Kalu dama wasu manyan jiga-jigan Jam’iyar APC mai mulki a jiya sun kaddamar da ofishin yakin neman sake zaben shugaba Muhammadu Buhari a karo na biyu wato a zaben 2019.

An dai kaddamar da ofishin ne a Mokola dake Ibadan a jahar Oyo

Haka kuma an lura a filin taron babu gwaunan jahar maici wato Abiola Ajimobi da sauran gwaunonin yankin yarbawa dama jiga-jigan Jam’iyar na wannan yankin.

A jawabin da ya gabatar a wurin taron, ministan na sadarwa wato Adebayo Shittu yace:

“Abinda shugaba Muhammadu Buhari yayi a cikin shekaru biyu da rabi kacal, gwaunatin da ta shude ta PDP batayi shi ba a cikin shekaru 16 datayi tana mulki a kasar. Haka kuma amma cikin wadannan shekaru biyu da rabin kacal shugaba Buhari ya samar da ayyukanyi sama da dubu dari biyu 200,0000 ga yayan Najeriyar baki daya “

You may also like