
Asalin hoton, Getty Images
Obita David Livingstone ya zargi ƴan sanda a arewacin Uganda da ƙin bibiyar zarge-zargen cin zarafi ta lalata
An bankaɗo yadda ake samun ƙaruwar cin zarafin ƴan mata a arewacin Uganda bayan wani rahoto da aka yi cewa a lokacin annobar korona adadin ƴan mata tsakanin shekara 10 zuwa 14 da ke samun juna biyu ya ninka fiye da sau huɗu. Sashen Binciken Ƙwaƙwaf na BBC Africa ya duba dalilin da ya sa ba a hukunta masu aikata ɓarnar.
Matashiyar wadda juna biyunta ya tsufa – ba ta wuce shekara 12 ba – ta kalli hannayenta yayin da shugaban ƙaramar hukumar ke tambayarta game da zuwanta ganin likita.
Tambaya ce da ya kamata ɗan uwa ya yi ta amma wannan juna biyun ya zo daban.
Yarinyar tana zaman kanta ne a wani ƙaramin gida da ke Lardin Kitgum kuma a kowane lokaci haihuwa za ta iya zuwa.
Sana’ar iyayenta ta rogo ta durƙushe a don haka suka koma ƙauyensu domin fafutukar neman kuɗi.
“An ƙyale ta a nan saboda nan ɗin ya fi zama kusa da makarantu,” in ji shugaban ƙaramar hukumar Obita David Livingstone.
“Amma abin takaicin, ɗakin da ke kusa da nata waje ne da mutane ke shaye-shaye. Wannan kaɗai ya jefa ta cikin ƙalubale da dama.”
Babu wanda ya san mahaifin jaririn da ke cikinta ko ma abin da ya faru.
‘Muna samun ƙararraki uku a mako ɗaya’
Wannan matashiyar kaɗai aka amince BBC Africa Eye ta naɗi hirarta, wadda kuma ba za mu ambaci sunanta ba saboda Mista Livingstone ya ce yana son ya wayar da kai game da matsalar cin zarafi ta hanyar lalata da ake samu a yankin.
“A mako ɗaya, muna samun ƴan mata kamar uku da aka lalata ƴan matancinsu. Wani lokacin idan aka kama masu aika-aikar, sai dai mu ƙulle su da igiya mu tafi da su, mu raka su zuwa ga ƴan sanda. Amma ba sa damuwa su bibiya.”
Ya siƙe da rashin hukunta masu laifin.
“Babu wanda zai iya tallafa wa wanda aka yi wa fyaɗe. A ganina, ina ganin akwai rauni a tsarin shari’ar,” in ji shugaban ƙaramar hukumar.
A cewar Hukumar Kula da harkokin lafiya ta Uganda, juna biyu tsakanin ƴan mata da shekarunsu ke tsakanin 10 zuwa 14 ya ƙaru da kashi 366 cikin 100 a tsukin kullen korona da ƙasar ta yi tsakanin Maris da Yunin 2020.
A babban asibitin yankin da ke Gulu, kusan kashi ɗaya bisa huɗu na ƴan matan da ke ƙasa da shekara 18 ne suka samu juna biyu.
Asalin hoton, Getty Images
Dr Baifa Arwinyo tana duba matasa masu juna biyu da suka faɗa hannun masu cin zarafi
Dr Baifa Arwinyo, shugaban sashen ɓangaren kula da lafiyar mata, ya ce: “Idan ina maganar ƴn mata da suka haihu, dukkansu an ci zarafinsu ta lalata. Matasa ne, bai kamata su kasance suna da juna biyu ba.
“Za ka ga ƴan mata da suka zama iyaye sun fi yawa cikin waɗanda suke mutuwa saboda matsala yayin naƙuda. Matsala ta fi afkuwa kan ƴan matan da ba su da shekaru da yawa.”
‘Cin zarafi wata dabarar yaƙi ce’
Ana tunanin daɗuwar cin zarafi ta lalata wata matsala ce da yaƙin shekara 20 da aka yi a arewacin Uganda ya haifar da ita.
Joseph Kony, Shugaban Lord’s Resistance Army, wata ƙungiyar ƴan tawaye da ke son hamɓarar da gwamnati.
Mayaƙansa sun yi ƙurin suna wajen azabtar da mutanen da suka yi garkuwa da su: yanke musu laɓɓa da hannaye da tilasta wa mutane yadda da abin da suke so ta hanyar jefa fargaba a zukatansu.
An ƙiyasta yara 40,000 ne aka sace ko aka tilasta musu zama sojoji ko yin lalata da su sannan mutum miliyan 1.7 suna zaune a sansanonin ƴan gudun hijra.
Ƴan tawayen sun fice daga Uganda a 2008 amma mummuman tasirin abubuwan da suka aikata har yanzu na nan, a cewar mai fafutukar kare haƙƙin bil adama Pamela Angwech, Daraktar Ƙungiyar Gulu Women Economic and Globalisation.
“Zama cikin irin wannan mummuman yanayi da wuraren da aka dasa nakiyoyi na da tasiri sosai kan al;umma. Mutane sun saba da ganin gawarwaki, mutane sun saba ganin mace-mace. Ana amfani da cin zarafi ta lalata a matsayin wata dabara da ƙungiyar LRA ke amfani da ita.
“Na bayyana hakan da matsayin yaƙin da ake fafatawa a jikin mace sannan macen ta zama filin daga.”
Mutane ƙalilan ne aka yi wa adalci saboda aikata muggan laifuka a lokacin yaƙin.
An gurfanar da wani kwamandan LRA, Dominic Ongwen a Kotun Hukunta Manyan Laifuka inda aka same shi da aikata laifukan yaƙi da cin zarafin bil adama 61 a Fabrairun 2021.
ICC na neman Kony ruwa a jallo amma har yanzu ba san inda yake ba.
Asalin hoton, Getty Images
Lauya Eunice Lakaraber Latim tana faɗakar da al’ummar yankin game da cin zarafin ƙananan yara
A cewar lauya Eunice Lakaraber Latim, da ke aiki a ƙungiyar Caritas, rashin tabbatar da adalci na ci gaba da samun wajen zama a arewacin Uganda har zuwa yanzu.
“Tasowa a Gulu, na ga yadda yara da dama ke fuskantar cin zarafi kuma akasarin iyayensu ba su da ikon neman adalcin da yaransu ke buƙata.”
‘Yarinyata na cikin ƙunci’
Ms Latim ta kai tawagar Africa Eye ga iyalin wata yarinya ƴar shekara uku da wani ɗan uwanta ya yiwa fyaɗe.
Mahaifiyarta ta gano lamarin ne bayan da ta lura tafiyar yarinyar ta sauya. Da ƴan sanda suka zo kama ɗan uwan nata, ta ce sun nemi kuɗin mota a wajenta domin kai shi ga hukuma.
“Ana kuma sa ran ciyar da fursunan,” in ji Ms Latim.
“Dole ka yi amfani da kuɗi idan kana son adalci. Dole ka biya kuɗin mai domin a je a kamo wanda ake zargi.
“Ya kamata ka samar musu da abinci matuƙar suna hannun ƴan sanda.”
An tsare wanda ake zargi tsawon wata shida amma saboda rashin bin wasu dokoki, aka ba shi beli. Mahaifiyar ba ta da kuɗin da za ta bibiyi lamarin.
Rahotanni daga ƴan sanda da likitoci sun tabbatar cewa yarinyar ƴar shekara uku ta kami da cuta mai karya garkuwar jiki.
“Yarinya ta har yanzu tana cikin ciwo, ko yanzu. Har yanzu ba ta warke ba,” in ji mahaifiyarta.
“Ya kamata a yanke masa hukuncin zaman gida yari. Ban so batun ya ƙare a haka ba.”
Ms Latim ya ce ba sabon abu bane ɓangaren shari’a ya gaza yin adalci inda ta ce sun samu mutane da yawa da suka rasa samun adalci.
“Akwai matsalar cin hanci sosai. Mutane ba sa jin tsoron aikata laifuka a nan saboda, sun ce idan kana da kuɗi, za ka fidda kanka. Abin da ke faruwa ke nan.”
Nacula Damalie, babbar jami’arin ƴan sanda a yankin Aswa, ta tabbatar da matsalolin da suka shafi yadda ake tafiyar da wasu ƙararrakin amma ta musanta cin hanci ya yi katutu.
“Bai kamata mu tambayi wanda aka yi wa fyaɗe kuɗi ba. Amma wani lokacin na san da cewa mai na iya ƙarewa. Eh.
“Da wannan matsala ta rashawa, ana yi wa jami’an ƴan sanda kallon masu cin hanci da rashawa, amma ba dukkansu ke karɓar cin hanci ba, kamar dai yake a sauran hukumomi. Muna da masu kyan hali da baragurbi.”
Ƙaramar ministar arewacin Uganda, Grace Freedom Kwiyucwiny ita ma ta tabbatar da matsalolin.
“Ba zan iya cewa babu matsalar cin hanci ba. Akwai matsalar. A dukkan matakai, har ma da matakan ma’aikatu,” in ji ta.
“Muna da dokokin cin zarafi ta lalata, akwai dokoki kan lalata tsakanin ƴan uwa amma mutane sai su zagaya su bai wa ƴan sanda cin hanci sai kuma ƴan sanda su ce, “Tor, ku je ku sasanta kanku a gida.’ Akwai ƙararraki da aka kai gaban kotu amma adadin ba su da yawa.”
Babu guda cikin waɗanda ake zargi a ƙararrakin da BBC Africa Eye ta yi bincike a kai da aka gurfanar gaban shari’a.