Yari yaƙi zuwa Zamfara duk da mutanen da aka kashe


Abdulaziz Yari, gwamnan jihar Zamfara na ɗaya  daga cikin gwamnoni 13 da suka gana da shugaban ƙasa Muhammad Buhari a mahaifarsa dake Daura.

Gwamnan wanda aka rawaito bai ziyarci jiharsa ba tun lokacin da aka bada labarin wasu ƴan bindiga sun kashe mutane 41.

Wasu ƴan bindiga ne suka kai hari kan ƙauyen Birane inda suka kashe mutane 41.

Jaridar Premium Times ta gano cewa gwamnan har zuwa ranar Alhamis bashi da masaniya akan abinda yafaru.

Jaridar tace lokacin da ta tuntubi kwamishinan yaɗa labaran jihar Sanda Danjari  a ranar Alhamis yace ba shi da tabbacin faruwar harin.

“Naji labarin a gidan rediyon Faransa da safiyar yau, amma har yanzu ban tabbatar ba.”yace.

An jiwo shi yana cewa ya yi kokarin yin magana da gwamna Yari kan batun harin amma abin yaci tura.

You may also like