An samu nasarar yiwa wata jaririya yar kasar Kodebuwa da aka haifa da kafa hudu da kuma laka biyu, tiyata a birnin cikago na Kasar Amurika.Yayin wani aikin tiyata mai sarkakiya wanda ya dauki tsawon sa’a 6 wanda likitoci 6 sukayi aikin.
Jariyar mai suna Dominique tana can tana murmurewa a hannun marikanta dake birnin illinoys na jihar cikago.Mutanen sun samu labarin halin da jaririyar take ciki ta hanyar shafin sada zumunta na facebook inda suka kudiri aniyar tallafa mata.
Dominique dai zata koma wurin iyayenta can kodebuwa da zarar ta gama murmurewa.