Yarinyar Data Mutu Ta Dawo Bayan shekaru Biyu


A jiya ne mazauna unguwar Masala na yankin Nndola na kasar Zambiya suka kaɗu iya kaɗuwa sakamakon ganin wata yarinya winnie da ake kyautata zaton cewa ta mutu tun shekaru 2 da suka wuce.

Ita dai winnie ta yi wata rashin lafiya daga nan kuma ta ce ga garinku. Daga nan aka mika ta zuwa mutuwari, inda aka mika ka ta ga iyayenta aka binne ta. Yanzu kuma bayan an yi kukan mutuwarta an gama, sai kuma ga ta ta dawo gida har take bayyana cewa: da ma fa bishiyar ayaba aka binne ba gawarta ba.

A halin yanzu dai lamarin yana hannun ‘yan sanda inda za a yi gwajin jini na DNA nata da na iyayenta, don a tabbatar da cewa, ‘yar tasu ce. Kuma iyayenta sun mika takardar shaidar haihuwa da mutuwar Winnie ga ‘yansanda, don su ci gaba da bincike a kan al’amarin.

You may also like