Yaro Dan Shekara 16 Ya Yiwa Yar Shekara 14 Fyade Har Takai Da Samun Ciki Wata kotun Majistire dake jihar Katsina ta bada umarnin a tsare wani matashi mai shekaru 16 Abdulmalik Yau, na kauyen Durbi Ta-kusheyi dake karamar hukumar Mani kan zargin yiwa wata yarinya yar shekara 14 fyade har takai ga ta samu ciki.

An gurfanar da mutumin da ake zargi kan aikata laifin fyade wanda ya saba da sashi na 283 na kundin shariar penal code. 

Mahaifin yarinyar Murtala Lawal shine ya shigar da korafi wajen yan sanda kamar yadda takardun karar suka nuna. 

Takardun shigar da karar sun kuma nuna cewa mutumin da ake zargi da kuma yarinyar dukkaninsu suna zaune ne a gida daya. 

Mai Shari’a Fadila Ahmad itace alkalin kotun, ta kuma fadawa mutumin da ake zargi cewa kotun bata da hurumin sauraren karar don haka ta bada umarnin a cigaba da tsare shi a gidan yara har sai lokacin da za a tura korafin zuwa kotun da ta dace. 

Mai Shari’a Fadila ta dage sauraran karar zuwa ranar 20 ga watan Yuli 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like