
Shekarun Haftom kusan biyar da haihuwa.
Sunansa “attajiri” a harshen Tigriyna amma nauyinsa bai wuce rabin yadda ya kamata ya kai ba.
A yayin da likita ya cire riga da wandonsa domin ganin hannaye da kafafunsa, mahaifiyarsa ta zuba ido tana kallon abin da ke faruwa.
Ba ta so ta fadi sunanta.
Wannan shi ne irin abin da ke faruwa na masifar yunwa da karancin abinci sakamakon yakin da aka kwashe shekara biyu ana yi a yankin Tigray da ke arewacin Ethiopia. Wata yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla ta sa an daina yaki amma ana ganin sakamakon yakin karara.
A watan Agusta, Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa yaro daya a cikin ko wadanne yara uku ‘yan kasa da shekara biyar a Tigray na fama da tamowa.
A yayin da sojojin gwamnatin tarayya da dakarun Tigray suke fafatawa, hukumomin Ethiopia ko dai sun takaita kai kayan agaji ko kuma sun hana kai wa baki daya zuwa yankin.
‘Hannu-rabbana’
Makda, wadda shekarunta suke daidai da na yakin da aka kwashe ana yi, ta kwanta a hannun mahaifiyarta Hiwot kamar yadda sauran jarirai suke yi.
Ta yamushe kuma cikinta ya kumbura.
Hiwot da ‘yarta Makda
“Abu ne mai matukar wahala samun abinci,” a cewar Hiwot. “Yana da matukar wahala ka samu abin da za ka ci ko da sau daya ne a kowacce rana.”
Sai dai jikin Makda ya ci gaba da yin tsanani tun bayan da aka kwantar da ita a asibiti.
“Diyata tana cikin wannan yanayi ne saboda an gaya mana cewa babu magani. Ba mu iya samun komai ba,” in ji Hiwot.
“Ko a lokacin da muka zo nan wurin a bara saboda irin wannan matsalar, ban iya samun komai ba kuma na tafi gida hannu-rabbana.”
Iyayen Haftom da Makda sun je Mekelle, babban birnin yankin Tigray, domin a kula da lafiyar ‘ya’yansu. BBC ta dauki hotunan bidiyo da kuma yin hira da su a watan da ya gabata.
Bayan watan Agusta, a yayin da dakarun gwamnatin tarayya suka kwace karin garuruwa, hukumomin Tigray sun amince su tsagaita wuta.
A cikin yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla a watan jiya, hukumomin birnin Addis Ababa sun ce za su aika da karin kayan agaji.
‘Kayan agaji ba sa wadata ko kadan’
Dr Kibrom Gebreselassie ya kwashe shekara 15 yana aikin fida a asibitin Ayder Referral Hospital.
Shi ne asibiti mafi girma a lardin da ke da mutane miliyan bakwai.
“Abu ne mai tayar da hankali ka rika ganin ‘ya’ya da iyayensu cikin mawuyacin hali a kowacce rana,” in ji Dr Kibrom.
“Yara da dama sun mutu a asibitinmu saboda da zarar yana fama tamowa, ba abinci kadai za ka ba su ba . Suna bukatar magunguna, sinadaran antibiotics, minerals… kuma ba mu da su a na.”
Ana kai musu wasu daga cikin abubuwan da suke bukata amma ko kusa ba su isa ba.
Dr Kibrom ya ce manyan motoci biyu na magungunan dakungiyar bayar da agaji ta International Committee of the Red Cross (ICRC) ta ba su sun isa Mekelle.
“Magungunan da muka samu ba su fi a bai wa rabin marasa lafiyar da ke nan ba kuma suna karewa cikin kwana guda,” in ji shi.
Marasa lafiyar da ba su samu taimako a kullum ba suna mutuwa.
“Idan ka kalli marasa lafiyar da ke fama da kansa, lamarin ya munanan. Babu inda ake yin gashi a gaba dayan yankin Tigray,” a cewar Dr Kibrom.
“Kowacce rana, kowanne mako da kuma kowanne wata halin da masu cutar kansa ke shiga yana ci gaba da tabarbarewa.”
Yunkurin kai agaji
Daga tsakiyar watan Nuwamba zuwa farkon watan Disamba, gwamnatin Ethiopia da kungiyoyin bayar da agaji sun yi kokarin tura manyan motoci fiye da 1,600 dauke da kayan agaji da suka hada da abinci, da gidaje na wucin gadi da magunguna, a cewar hukumar bayar da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya.
Ita kanta ICRC ta ce ta aika akalla manyan motoci 38 dauke da kayan agaji zuwa Mekelle tun daga tsakiyar watan Nuwamba, kuma za ta aika da karin kayan agaji.
“Dukkan kungiyoyin bayar da agaji suna yin kokari sai dai hakan bai isa ba idan aka yi la’akari da yawan mutanen da ke bukatar agajin,” in ji Jude Fuhnwi, kakakin ICRC a Ethiopia.
Asalin hoton, WFP
Shirin World Food Programme ya ce ya “zage dantse” wajen kai kayan agaji Tigray tun bayan da aka kulla yarjejeniyar zaman lafiya
Masu bukatar agajin suna da matuka yawa.
Shirin World Food Programme (WFP) na Majalisar Dinkin Duniya yana so ya ba da agajin gaggawa ga akalla mutum miliyan biyu da dubu dari daya a Tigray ciki wata shida.
“An samu ingantuwar lamura da dama tun bayan kulla yarjejeniyar zaman lafiyar ,” in ji Claude Jibidar, wakilin WFP kuma daraktanta a Ethiopia.