Yau Alhamis Najeriya Zata Kaddamar Da Shirin Fara Fitar Da Doya Zuwa Kasashen Turai 


Hakkin Mallakar Hoto:Premium Times

Gwamnatin Tarayyar Najeriya tace zata kaddamar da shirin fara kai doya zuwa kasashen Turai. 

Doya abinci ce da ake ci a Najeriya kuma a ke noma ta a wasu yankuna na kasar. 

 Ministan Aiyukan Noma, Audu Ogbeh, ne   ya bayyana shirin na fara safarar doya zuwa kasashen Turai ,lokacin da yake ganawa da yan jaridun dake fadar shugaban Kasa bayan taron majalisar zartarwa ta kasa, da mukaddashin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.
Mista Ogbeh yace a kason farko na shirin za  a tura da tan 70 na doyar zuwa kasar Burtaniya.

Ministan yace bikin na yau shine kaddamar da shirin a hukumance, amma tuni wani kason na doyar ya isa birnin New York na kasar Amurika ranar 16 Ga Yuni, 2017.

 Ogbeh yace a kididdigar Hukumar Kula da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, FAO,”Najeriya ce take samar da kaso 60 cikin dari na doyar da ake samarwa a duniya.”

Yace doyar da ake nomawa a Najeriya  ana bukatar ta a kasashen duniya sosai inda yakara da cewa “abin kunya ne ace ba a samunta  a wadancan kasuwanni.”
“Bama iya cinye doyar da muke nomawa yawancin ta rubewa take, “yace. 

Ministan yace domin maganin matsalar rubewar doyar, ma’aikatarsa na kokarin samar da na’urar sanyi mai amfani da hasken rana. 

You may also like